Matthew 13

Misali na Mai Shuka

1A ranan nan sai Yesu ya fita daga gida ya je ya zauna a bakin tafkin. 2Taron mutane mai yawan gaske suka taru kewaye da shi har ya kai sai da ya shiga jirgin ruwa ya zauna, yayinda dukan mutane suka tsaya a gaci. 3Saʼan nan ya faɗa musu abubuwa da yawa cikin misalai, yana cewa: “Wani manomi ya fita don yǎ shuka irinsa. 4Da yana yafa irin, waɗansu suka faffāɗi a kan hanya, tsuntsaye kuwa suka zo suka cinye su. 5Waɗansu suka faffāɗi a wurare mai duwatsu, inda babu ƙasa sosai, nan da nan kuwa suka tsira, da yake ƙasar ba zurfi. 6Sai dai da rana ta ɗaga, sai tsire-tsiren suka ƙone, suka kuma yanƙwane domin ba su da saiwa sosai. 7Waɗansu irin suka fāɗi a cikin ƙaya, ƙayan kuwa ta yi girma ta shaƙe su. 8Har wa yau, waɗansu irin suka faffāɗi a ƙasa mai kyau, inda suka ba da amfani-riɓi ɗari, sittin ko kuma talatin na abin da aka shuka. 9Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”

10Almajiran suka zo wurinsa suka yi tambaya, “Me ya sa kake wa mutane magana da misalai?”

11Ya amsa ya ce, “Sanin asirin mulkin sama kam, ku aka ba wa, amma ba su ba. 12Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, zai kuwa samu a yalwace. Duk wanda kuma ba shi da shi, ko ɗan abin da yake da shi ma, za a karɓe. 13Abin da ya sa nake musu magana da misalai ke nan:

“ ‘Ko da yake suna ƙallo, ba sa gani;
ko da yake suna saurara, ba sa ji ko su gane.’
14A kansu ne aka cika annabcin Ishaya cewa:

“ ‘Za ku yi ta ji amma ba za ku taɓa ganewa ba;
za ku yi ta ƙallo amma ba za ku taɓa gani ba.
15Gama zuciyar mutanen nan ta taurare;
da ƙyar suke ji da kunnuwansu,
sun kuma rufe idanunsu.
Da ba haka ba, mai yiwuwa su gani da idanunsu,
su kuma ji da kunnuwansu,
su gane a zuciyarsu,
su kuwa juya, in kuma warkar da su.’
Ish 6.9, 10

16Amma idanunku masu albarka ne domin suna gani, haka ma kunnuwanku domin suna ji. 17Gama gaskiya nake gaya muku, annabawa da mutane masu adalci da yawa sun yi marmarin ganin abin da kuke gani amma ba su gani ba, su kuma ji abin da kuke ji amma ba su ji ba.

18“To, ku saurari maʼanar misali na mai shukan nan. 19Duk saʼad da wani ya ji saƙo game da mulkin bai kuwa fahimce shi ba, mugun nan yakan zo yǎ ƙwace abin da aka shuka a zuciyarsa. Wannan shi ne irin da ya fāɗi a kan hanya. 20Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a wuraren duwatsu kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, nan da nan kuwa yǎ karɓe ta da murna. 21Sai dai da yake ba shi da saiwa, yakan ɗan jima kaɗan kawai. Da wata wahala ko tsanani ya auko masa saboda maganar, nan da nan sai yǎ ja da baya. 22Wanda ya karɓi irin da ya fāɗi cikin ƙaya kuwa, shi ne mutumin da yakan ji maganar, sai dai damuwoyin rayuwan nan da jarabar arzikin duniya sukan shaƙe shi, yǎ sa maganar ta kāsa amfani. 23Amma wanda ya karɓi irin da ya fāɗi a ƙasa mai kyau, shi ne mutumin da yakan ji maganar yǎ kuwa fahimce ta. Yakan ba da amfani wani riɓi ɗari, sittin, ko talatin na abin da aka shuka.”

Misali na Ciyayi

24Yesu ya ba su wani misali: “Mulkin sama yana kama da wani da ya shuka iri mai kyau a cikin gonarsa. 25Amma yayinda kowa yake barci, abokin gābansa ya zo ya yafa ciyayi a cikin alkamar, ya tafi abinsa. 26Saʼad da alkamar ta tashi ta yi kawuna, sai ciyayin ma suka bayyana.

27“Bayin mai gonar suka zo wurinsa suka ce, ‘Ranka yǎ daɗe, ashe, ba iri mai kyau ka shuka a gonarka ba? To, ina ciyayin nan suka fito?’

28“Sai ya ce, ‘Abokin gāba ne ya yi wannan.’

“Bayin suka tambaye shi suka ce, ‘Kana so mu je mu tuttumɓuke su?’

29“Ya amsa ya ce, ‘Aʼa, don kada garin tuttumɓuke ciyayi, ku cire har da alkamar. 30Ku ƙyale su su yi girma tare sai lokacin girbi. A lokacin zan gaya wa masu girbi: Da fari ku tara ciyayin ku kuma ɗaure su dami-dami don a ƙone; saʼan nan ku tara alkamar ku kuma kawo su cikin rumbuna.’ ”

Misalai na Ƙwayar Mustad da na Yisti

31Ya ba su wani misali ya ce: “Mulkin sama yana kama da ƙwayar mustad, wadda mutum ya ɗauka ya shuka a gonarsa. 32Ko da yake ita ce mafi ƙanƙanta cikin ƙwayoyinku, duk da haka saʼad da ta yi girma, takan zama mafi girma cikin tsire-tsiren lambu ta kuma zama itace, har tsuntsayen sararin sama su zo su yi sheƙa a rassansa.”

33Har yanzu ya ba su wani misali ya ce: “Mulkin sama yana kama da yisti wanda mace ta ɗauka ta kwaɓa garin alkama mai yawa, har sai da yistin ya garwaye yistin duka.”

34Yesu ya faɗa wa taron dukan waɗannan abubuwa cikin misalai; bai faɗa musu kome ba, sai tare da yin amfani da misalai. 35Ta haka aka cika abin da aka faɗa ta wurin annabi cewa:

“Zan buɗe bakina da misalai,
zan faɗi abubuwan da suke ɓoye tun halittar duniya.”
Zab 78.2

An Bayyana Misali na Ciyayi

36Saʼan nan ya bar taron ya shiga gida. Almajiransa kuwa suka zo wurinsa suka ce, “Bayyana mana misalin ciyayin nan a gona.”

37Ya amsa ya ce, “Mai yafa irin mai kyan nan, shi ne Ɗan Mutum. 38Gonar kuwa ita ce duniya, irin nan mai kyau kuwa suna a matsayin ʼyaʼyan mulkin. Ciyayin nan kuma su ne ʼyaʼyan mugun nan, 39abokin gāban da yake shuka su kuwa, Iblis ne. Lokacin girbi kuma shi ne ƙarshen zamani, masu girbin kuwa su ne malaʼiku.

40“Kamar yadda aka tattara ciyayin aka kuma ƙone a wuta, haka zai zama a ƙarshen zamani. 41Ɗan Mutum zai aiki malaʼikunsa, su kuwa cire daga mulkinsa kome da yake jawo zunubi da kuma duk masu aikata mugunta. 42Za su jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora. 43Saʼan nan masu adalci za su haskaka kamar rana a mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yǎ ji.”

Misalai na Ɓoyayyiyar Dukiya da na Luʼuluʼu

44“Mulkin sama yana kama da dukiyar da aka ɓoye a gona. Da wani ya same ta, sai yǎ sāke ɓoye ta, saʼan nan cikin farin cikinsa yǎ je yǎ sayar da duk abin da yake da shi yǎ sayi gonar.

45“Har wa yau dai, mulkin sama yana kama da ɗan kasuwa mai neman luʼuluʼai masu kyau. 46Da ya sami dutse guda mai daraja sosai, sai ya tafi ya sayar da dukan abin da yake da shi ya saye shi.

Misali na Taru

47“Har yanzu, mulkin sama yana kama da tarun da aka jefa cikin tafki yǎ kamo kifi iri-iri. 48Da tarun ya cika, masuntan suka jawo shi gaci. Sai suka zauna suka tattara kifi masu kyau a kwanduna, amma suka zubar da marasa kyau. 49Haka zai kasance a ƙarshen zamani. Malaʼiku za su zo su ware masu mugunta daga masu adalci 50su kuma jefa su cikin wuta mai zafi, inda za a yi kuka da cizon haƙora.”

51Yesu ya tambaye, su ya ce, “Kun gane dukan waɗannan abubuwa?”

Suka amsa, “I.”

52Saʼan nan ya ce musu, “Saboda haka duk malamin dokokin da ya horu game da koyarwar mulkin sama, yana kama da maigida wanda yakan fitar daga ɗakin ajiyarsa sababbin dukiya da kuma tsofaffi.”

Rashin Ganin Darajar Annabi

53Saʼad da Yesu ya gama ba da waɗannan misalai, sai ya ci gaba daga can. 54Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majamiʼarsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka? 55Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ʼyanʼuwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba? 56Duk ʼyanʼuwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?” 57Sai suka ji haushinsa.

Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”

58Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

Copyright information for HauSRK